Gane Mini Hanya 9/10/2021: Yadda ciwon miƙewar gaba ya hana ni aure’
An wallafa
Latsa hoton sama domin sauraren shirin:
Maza masu fama da lalurar amosanin jini sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki, ta hanyar samar da cibiyoyin Nazari don sama musu maganin cutar sakamakon barazanar mutuwar mazakuta da suke fuskanta.
Wani mai fama da irin wannan matsalar ya shaidawa BBC, idan lalurar ta motsa masa yakan shiga tashin hankali da radadin ciwo sakamakon mikewar da mazakutarsu ke yi da tsananin ciwo.
Matashin ya shaidawa wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji cewa matsalar ta sanya ya gagara yin aure.