Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mai fafutukar kare hakkin mata a Somaliya ta ce an yi amfani da Facebook wajen hana ta bayyana ra'ayinta
- Marubuci, Daga Layla Mahmood
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, 'Yar Jarida
- An wallafa
"Ba mu kashe ki ba a Somalia kana yanzu kin samu 'yanci a Birtaniya, amma za mu toshe ki a shafin Facebook" - an yi wannan gargadin ne ga wata mai rajin kare hakkin mata 'yar kasar Somalia mai zama a Birtaniya.
Hanna Paranta (da aka fi sani da suna Hanna Abubakar a shafukan intanet), wacce ke taimaka wa wadanda aka ci zarafi da kuma yi wa fyade ta hanyar amfani da shafin Facebook, ta ce wadanda ke yaki da ayyukan da take yi sun kira ta a wayar salula shekara daya da ta gabata.
Ta ce an jirkita yadda sashen nan na Facebook da ake kai rahoto da aka kirkira domin tabbatar da samar da wani gurbi da babu cin zarafi ko batanci ke amfani inda yake yin akasin haka - an yi amfani da sashen a matsayin wani makami na yakarta ta shafin na Facebook.
Shafinta na Facebook na da mabiya fiye da 130,000, amma tana da yakinin cewa 'yan kasar Somalia da ke tsananin adawa da bai wa mata 'yancin daidato sun kai rahoton ta ga kamfanin Facebook a wani yunkuri na ganin an rufe shafinta.
Kamfanin Facebook ya ce ana bayar da muhimmanci tare da tsananin bincike kan rahoton.
Guba a cikin abinci
Miss Paranta, mai shekaru 44, wacce daga Somalia ne suka koma kasar Sweden lokacin tana da shekara bakwai, yanzu ta koma Birtaniya da zama.
A can ne ta fara aikin taimaka wa al'umma kuma a cikin shekaru goma da suka gabata ta kasance mai fafutikar kare hakkin mata.
Ta fara taimaka wa wadanda aka ci zarafinsu a gidaje da kuma yi wa fyade, a tsakanin al'ummar kasar Somalia mazauna Birtaniya - kuma ta yi suna a kasar ta Somalia inda ta kasance cikin kungiyoyin bayar da tallafi da dama - wani abu da ya fusata kungiyoyi masu ra'ayin gargajiya a kasar ta Musulmai.
A duk lokacin da za ta je kasar Somalia a kodayaushe takan tafi da masu tsaron lafiyarta, kana a ziyararta ta baya-bayan nan a cikin watan Satumbar shekarar 2020, wani ya yi yunkurin saka guba a abincinta a otal din da ta sauka a Mogadishu babban birnin kasar.
Wasu gungun masu rike da makamai sun yi yunkurin sace ta - masu tsaro lafiyarta ne suka shiga tsakani sannan mutanen suka gudu.
A lokacin da ta dawo ne ta aka bugo mata waya, kuma tun daga wannan lokacin ne kamfanin Facebook ya rika tsaurara mata ko kuma rufe shafinta - kuma ta yi amanna cewa wadanda suka kai kukansu na son a rufe shafin nata baki daya.
Duk da koken da ta mika game da batun ga Facebook, tana tunanin kamfanin ya gaza ganowa tare da duba rahotannin karyar.
Kuma Mis Paranta na ganin cewa mutane da dama sun hada kai sun kai mata hari ne ta Facebook.
'Haramci a fakaice'
"Na fara tuntubar kamfanin na Facebook a cikin watan Disamba. Na shaida musu komai cewa wadannan mutane na so a rufe shafina kana sun aike min da barazana, amma babu wanda ya saurare ni," in ji Mis Paranta.
Ta yi amanna wadanda suke da hannu wajen kai koken nata "suna da kungiya a manahajar aikewa da sakonni da Facebook mai mambobi fiye da 300, inda suke hada kai suna kai hari da kuma kai rahoton mutane".
Wata mai goyon bayan Mis Paranta ta shiga cikin kungiyar kuma ta aiko da hoton da ta dauka na musayar bayanan da ake yi a ciki.
Wasu daga cikin hotunan sun nuna yadda mutane ke tattauna yadda za su yi su samu nasarar hana Mis Paranta amfani da shafin Facebook kana suna kokarin cire ta daga shafin YouTube.
Ta fusata cewa kamfanin na Facebook ya toshe shafinta ba tare da fara gudanar da cikakken bincike ba.
Tattaunawarta da kamfanin ita ma ta kasance cikin damuwa: ana yawan hada ta da sassa daban-daban, ko kuma a bar ta tana magana da na'ura mai kwakwalwar da aka saita.
Bayan da BBC ta tuntubi kamfanin na Facebook don jin martanin da zai mayar game da wadannan zarge-zarge, Miss Paranta ta ce an janye wasu daga cikin kuntatawar da aka yi wa shafin nata a cikin watanni kadan da suka gabata, kamar su bangaren daukar faifen bidiyo kai tsaye.
Mai magana da yawun kamfanin Facebook ya bayyana cewa a yayin da kamfanin ya amince a rika tattauna muhimman abubuwa, bai amince wa mutane su rika "cin zarafi ko kuma zagin sauran mutane a shafin Facebook ba".
"Mun cire wasu abubuwan da suka saba ka'ida daga ciki, wadanda aka sanar da mu akai, kana bincikenmu ya gano cewa babu sauran haramci da suka rage a shafin mai fafutikar."
Aamma kuma, Miss Paranta ta bayyana cewa har yanzu akwai "haramci na fakaice", da hakan ke nufin abubuwan da take wallafawa ba sa bayyana akai-akai a idanun mabiyanta.
Kana ba ta iya samun sabbin mabiya da kuma tantance shafinta da shudiyar alama mai lankawasa.
Zuga wasu mata
Amma su wanene suke yawan kai karar shafinta ga kamfanin na Facebook? Wani abin mamaki, akasarinsu mata ne.
Amina Musse Wehelie, 'yar jarida kuma mai fafutikar kula da lafiyar kwakwalwa ta gano cewa akwai wani babban mai fada a ji a kasar Somalia da ke jagorantar wadannan kungiyoyi masu kai kara a Facebook.
Shi da sauran wasu mazan Somalia, na ta jan hankalin matan kasar da ke zaune a kasashen waje don yin amfani da su a yakin da suke yi da sananniyar mai fafutikar, a cewarta.
"Sukan samu matan da daukar dawainiyar 'yayansu su kadai ta bas u da wata sana'a ko 'yanuwa a kusa. Matan da ke zaman kadaici, kana suna jin sun yi nisa da kasarsu ta asali [Somalia].
"Sukan fada musu cewa za su iya 'yin komai' kana cewa suna da "muhimmanci." Daga nan, sukan ja hankalinsu wajen yin aiki tare da su da kuma biyan su kudi."
A yayin da wannan gangami yada labaran karya a shafukan sada zumunta game da 'yar kasar ta Somalia mai fafutika - lamarin ya kasance mai muni ga Mis Paranta a cikin watanni da suka gabata.
"Shugaban gungun mutanen sun fara cewa ina fataucin sassan jikin mutane. Daga nan kuma y ace ina sayar da matan Somalia a matsayin karuwai, kana yanzu kuma yana cewa ina kokarin mayar da Musulmai 'yan kasar Somalia zuwa Kiristoci," ta ce.
Irin wannan farfagandar ta kara karfin gwuiwar kar karar shafin Mis Paranta na Facebook, tun da yanzu mutane da dama na kallon ta a matsayin mai aikata muggan laifuka wanda ya sa ba zai yiwu da ci gaba da gudanar da aikinta ba.
Mis Wehelie da Miss Paranta na ganin harshe shi ne babban dalilin da ya sa kamfanin Facebook ya kasa gudanar da bincike game da labaran karya - kana suna ganin ba a dauke su da muhimmanci ba saboda su mata ne daga al'ummar kasar Somalia.
"Ra'ayina shi ne a lokacin da wadannan mutane ke amfani da harshensu, kamfanin Facebook ba ya fahimta," in ji Mis Wehelie, tana mai bayyana cewa Facebook na bangaren da ke fassara harshen Somalia ba ya aiki sosai.
'Yar jaridar ta yi amanna cewa hanya daya da za a iya gyara wannan za ta kasance cewa kamfanin Facebook ya dauki karin wasu 'yan kasar ta Somalia aikin fassara.
Mis Paranta fna fargabar cewa za a cigaba da kai wa shafinta hari, kana mutanen da ta taimaka wa za su kasance ba su da wurin da za su dosa.
Layla Mahmood 'yar jarida ce mai bincike da ke zaune a birnin London