Britney Spears: Ruɗanin da ta shiga bayan miƙa ragamar rayuwarta a hannun mahaifinta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Fitacciyar mawakiyar nan ta Amurka Britney Spears ta yi kira a kawo karshen "cutar" da ake mata a bangaren kasuwancinta da abin da ya shafi rayuwarta, kamar yadda ta shaida wa wata kotu a birnin Los Angeles.

"Ina so a dawo mini da rayuwata", in ji ta.

Duka sha'anin gudanar da rayuwar mawakiyar na hannun wanda shari'a ta naɗa ya rika tafiyar mata da su kan wani tsari da ake kira "lura da lamuran masu rauninmu" a 2008 lokacin da ta samu matsala a kwakwalwarta.

Kotun ta bai wa mahifinta Jamie Spears damar ci gaba da tafiyar da rukunin gidajenta da kuma al'amuran rayuwarta.

Amma daga baya mawakiyar ta nemi a karbe wannan iko daga hannun mahaifinta.

Wani gangami da masoyanta suka assasa mai taken #FreeBritney, suna son a mayar wa da mawakiyar 'yancinta game da rayuwarta.

Hankali ya kara komawa kan wannan umarnin na kotu a 2021, bayan samun wani bayani kan Britney Speras wanda ya mayar da hankali kan rikicin da ke tsakanin mawakiyar da mai lura da lamuranta.

Mece ce dokar lura da mutanen da ba za su iya lura da kansu ba?

Dokar lura da mutanen da ba za su iya lura da kansu ba wani umarni ne da kotu ke bayarwa domin lura da wadanda suke da matsalar kwakwalwa da ba za su iya lura da kansu ba, kamar wadanda suka samu cutar mantuwa da dai sauran cutuka na kwakwalwa.

Dokar da ke kan Spears ta rabu kashi biyu - daya a kan rukunin gidajenta da kuma harkokinta na kudi, sai kuma wadda ke ita kanta. Karkashin wannan bayanin na kotu, Spears ba ta da iko kan dukiyarta tun 2008.

Jamie Speras shi ke lura da duka bangarori biyun da kotu ta bayar da umarni a kansu, amma a 2019 ya ajiye aikin lura da dukiyarta ta da ita kanta saboda rashin lafiyar da ya yi fama da ita. Sai Jodi Montgomery ya maye gurbinsa na wani dan lokaci, amma Britney ta nemi hakan ya zama na din-din-din.

Wani bayanin kotu na sirri da jaridar News York Times ta samu ya nuna cewa, mawakiyar ta nuna rashin jin dadinta a wannan lokacin sama da a baya. Sun kuma nuna rashin dacewa da dokar lura da bangaren rayuwarta da aka matsa sosai a kai, kan abin da ya shafi saurayin da take kulawa zuwa launin da madafar abincinta zai kasance.

"Abin da take gani shi ne wannan dokar ta matsa mata," mai binciken kotu ya rubuta a wani rahoton 2016. Wannan dokar ta mamaye komai na Spears.

A watan Nuwambar 2020, wani alkali ya cire Mista Spears tare da sanya kamfanin hada-hadar kudade na Bessemer Trust domin ci gaba da tafiyar da rukunin gidajejnta.

Bayan wata guda, alkalin ya kara tsawaita wa'adin Mista Spears na lura da 'yarsa har zuwa watan Satumba 2021.

Saboda me aka amfani da dokar lura da wadanda ba za su iya lura da kansu ba?

Spears ta fara wasu ɗabi'u na daban a 2007 bayan mijinta Kevin Federline ya sake ta an kuma kwace 'yayansu biyu daga hannunta.

An yi ta samun koke-koke daga mutane daban-daban kan matsalar kwakwalwarta, yayin da ta rika yin kanun labarai da kanta a aske.

Sau biyu aka kwantar da ita a asibiti a 2008, a lokacin ta yi zargin cewa an raba ta da 'yayanta.

A wannan lokacin ne aka kafa dokar lura da ita ta wani dan lokaci, kuma a hankali aka rika kara tsawaita ta har na kusan shekara 10, duk da cewa babu ko bangare daya na cikin dokar da aka bai wa jama'a.

A 2018, Spears ta samu sama da dala miliyan 59 in ji jaridar Business Insider, kuma ta biya dala miliyan 1.1 kan dokar lura da ita.

Me gangamin neman sakin Britney ya kunsa?

A 2009 ne aka fara gangamin neman sakin Britney kamar yadda New York Times ta ruwaito, wanda magoya bayanta suka nuna kin amince wa da shi.

A 2019 bayan ta soke zamanta na Las Vegas tare da zuwa duba lafiyarta da ta mahaifinta, sai aka sake waiwayar gangamin.

Wasu daga cikin magoya bayanta sun yi amannar cewa an matsa mata ne domin bin wannan dokar, ta kuma nemi fadar White House ta kawo karshen wannan dokar da aka sa mata,kokn da aka shigar tare da sanya hannun mutane dubbai.

Mafi yawan wannan gangamin ana yin sa ne a wajen kotun da ake sauraren kararta, Paris Hilton, Bette Midler da Miley Cyrus.

Da yawan fitattun mutanen sun nuna goyon bayansu kan gangamin.

Me Britney Spears ta ce game da wadannan abubuwa?

Sama da shekaru mawakiyar ba ta taɓa cewa komai ba kan wannan batu - duk kuwa da ce-ce-ku-cen da batun ke janyo wa a intanet.

Wasu da yawa sun yi amannar za a iya aika sako ta kafafen sada zumunta a boye.

A farkon wannan shekarar ne lauyan mawakiyar ya bukaci ta je ta yi wa kotu bayani kai tsaye kan wannan dokar da aka sanya mata.