Yadda manoma suka koma ƴan gudun hijira a Zamfara
An wallafa
Latsa alamar lasifika domin sauraren rahoton Awwal Janyau
Hare-haren ƴan bindiga da masu fashin daji a kauyukan jihar ya tilastawa daruruwan manoman kauracewa gonakinsu inda suka warwatsu zuwa wasu manyan birane domin samun mafaka.
Duk da a watanni baya wasu sun koma kauyukansu saboda zaman lafiyar da aka samu sakamakon sulhun da gwamnati ta ce ta yi da yan fashin daji da suka addabe su, amma akwai wadanda suka hakura da manyan gonakinsu a kauye kuma suke fargabar komawa gida.