Cape Town: Yadda Zikirin Musulunci ke daƙile rikicin ƴan daba da shaye-shaye a Afirka Ta Kudu

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Wata tawagar malaman addinin Musulunci a Afirka Ta Kudu ta shafe shekara uku tana wani ƙoƙari na yaɗa zaman lafiya a garin Manenberg da sauran yankunan birnin Cape Town da ake fama da matsalar ƴan daba da masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Mai ɗaukar hoto Shiraaz Mohamed ya bi tawagar yayin wata ziyarar mako-mako da take kaiwa:

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Yawanci da yammacin ranakun Alhamis malaman na zuwa yankunan da 'ƴan daban suke a Cape Town don gudanar da zikiri.
A taron zikirin ana yawan ambaton Allah da yi wa Annabi salati.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Waɗanda suke shirya taron sun ce a cikin shekara uku da suka gabata ba a taɓa samun rikicin ƴan daba ba a tsawon sa'a ɗaya da rabi na lokutan zikirin.
Yawanci a kan samu mutum 100 zuwa 400 da suke halarta. Akwai wani nau'in ibada da ake yi da zummar neman kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka shafi jinsi - wata babbar matsala a Afirka Ta Kudu - inda kusan mutum 2,000 ke halarta.
"Ba yawan mutanen da suke halarta ba ne abin dubawa. Abu mafi muhimmancin shi ne cewa duk da yanayin da aka dinga samun kai a ciki, ana samun damar yin zikirin ba tare da tsayawa ba a cikin shekara uku da suka wuce," a cewar Sheikh Mogamad Saalieg Isaacs.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Manenberg gari ne da aka ƙirƙira a lokacin gwamnatin da ke yaƙi da wariyar launin fata a shekarun 1960 don mutane ruwa biyu masu matsakaicin hali.
A wancan lokacin na mulkin farar fata ƴan tsirari sun ware sauran ƙabilu da tursasa musu zama a wasu yankunan, inda suke barin fararen fata Turawa kawai su zauna a manyan birane.
An yi ƙiyasin cewa akwai mutum 52,000 a garin Manenberg, waɗanda yawancinsu Kiristoci ne da mutanen da ba su da aikin yi masu yawa, ga talauci da aikata miyagun laifuka da kuma dabanci.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
A yanzu haka yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gungun ƴan daba biyu tana aiki, sakamakon rikicin da aka sha tafkawa tsakaninsu - duk da cewa awanni kaɗan kafin a fara zikirin an yi harbe-harbe a waɗannan gidajen, kuma a ƙarshen mako an kashe maza huɗu a wasu harbe-harbe da aka yi tsakanin gungun ƴan daban a kusa da Mitchells.
Masu shirya zikirin suna jin cewa ba za a taɓa samun wata hanya ta haƙiƙa ta kawo ƙarshen rikicin ba, kuma gwamnati ba ta yin wani ƙoƙari na magance shi.
Sheikh Issacs na ganin tattaunawa da dukkan shugabannin addinai daban-daban na yankin ita ce hanya ta farko mai ma'ana: "Laifi ba shi da addini ko a ina a kan samu masu aikata shi."
Yana kuma ganin cewa ya kamata hukumomi su kawo karshen cunkoson da ke akwai - su taimaka wa mutane su matsa zuwa wasu sassan maimakon ci gaba da gine-gine a cikin yankin birnin, a kuma kara samar da jami'an tsaro a ko ina.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Yawancin Musulmai a fadin duniya na yin zikiri kuma shi sautin zikiri ya fita daban. An fi gabatar da shi bayan faduwar rana da kuma lokacin Sallar Magariba.
Yankin Cape Malays, ya ƙunshi mutanen yankin Asiya ne, wadanda suka kwashe shekaru a Afrika Ta Kudu, kuma suna da tsarin sautinsu na daban.
Wasu mabiya addinin Kirista da ke zaune a birane kan halarci zikirin - su rika kallon yadda ake gudanar da shi daga gidajen maƙota.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Sheikh Sameeg Norodien shi ma na daga cikin masu shirya zikirin, yana dafa abinci ga masu gudanar da shi.
Akwai wata al'ada da ake da ita a birnin Cape, wadda mutane ke bayar da abubuwan ci masu dadi kyauta bayan taruka, a mafi yawan lokuta, ana kiranta "niyaz".
Amma a yankin Manenberg wata hanya ce ta kore talauci, bai wa masu zikirin abinci da zafinsa bayan gama zikirin.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
A 2015 ne hukumomi suka ce yakin Manenberg ya zama "yankin mai hadari" saboda watannin da aka kwashe ko motar asibiti ba a bari ta shiga yankin sai dai inda rakiyar 'yan sanda.
Amma a yanzu, manyan 'yan daban a wasu yankunan na taimaka wa malaman addinin Musulinci su shimfida tabarma lokacin da za a fara gabatar da zikirin, in ji Sheikh Isaacs.
"An samu wani lokaci tsakanin 2018 da 2019 da rikici suka ragu a Manenberg musamman a lokutan da muke da zikiri," in ji Sheik.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Har kyaututtuka 'yan sandan yankin Manenberg suka bai wa masu shirya zikirin saboda rawar da ya riƙa takawa na rage tashe-tashen hankula a yankin.
Wani dan gajeren ƙuduri ne da masu hada zikirin ke da shi na kawo zaman lafiya da nutsuwa da kwanciyar hankali a yankin birnin, amma dogon burinsu shi ne hada kai da masu ruwa da tsaki wajen ganin an fatattaki sai da muggan kwayoyi da kuma harkokin daba a yankin.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
Ana yawan yi wa yara gargadi game da sharrin miyagun ƙwayoyi tare da ba su ƙwarin gwiwar su riƙa shiga zikiri domin kaucewa faɗawa hanya mara kyau.
Ana cewa mabiya addinin Kirista ma na girmama zaman zikiri wanda masu shirya wa ke nuna yadda Musulmai ke rayuwa cikin zaman lafiya kuma ba masu son tahsin hankali ba ne.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
An gayyato malamai ya yi bayani a kowace ranar Alhamis. A nan Sheik Hasan Pandy ne ke bayani kan muhimmancin mahaifiya.
Mai bayanin yana amfani da amsa kuwwa ne, domin sakon ya isa ko ina - maganganu da suka shafi daidaiton jinsi zuwa yaƙi da shan miyagun kwayoyi - kowa ya zama ya ji me ake fada.
Masu shirya wannan zama na gayyato malamin Kirista a wasu lokutan shi ma ya zo ya yi bayani.

Asalin hoton, BBC/Shiraaz Mohamed
"Zikiri ya samar da kwanciyar hankali a Manenberg," in ji Sheik Isaacs.
"Muna zaman zikirin ne sau daya a sati. da za mu iya gabatar da shi a kullum da ya samar da sakamako mai ban mamaki, amma saboda kayan aikin da ake bukata ba za mu iya ba."
Dukkan hotuna na da haƙƙin mallaka










