Zaɓen Amurka na 2020: Ko sai kotu ta shiga tsakani ne?

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan takarar shugabancin Amurka ƙarƙashin Jam'iyyar Democrat, Joe Biden, ya kama hanyar lashe zaben ƙasar, amma abokin karawarsa Donald Trump na ƙalubalantar ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa a jihohi huɗu na ƙasar.
Me zai faru?
Ga abin da masana shari'a ke cewa.

Ko ya kamata a san sakamakon zaɓen a yanzu?
Eh kuma a'a. Akasari, a duk lokacin da aka ga ɗan takara na kan gaba ba tare da binsa a baya ba, manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka na ayyana mutum a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Wannan na faruwa ne washe gari da safe bayan zaɓe.
Sai dai wannan sakamakon zaɓen ba wanda aka fitar a hukumance ba ne, hasashe ne kuma asalin sakamakon yana ɗaukar ranaku kafin a bayyana shi.
Sai dai irin ƙuri'un da aka jefa a wannan shekara musamman waɗanda aka kaɗa ta akwatin gidan waya na nuni da cewa sakamakon zai ɗauki lokaci, musamman ganin cewa wasu jihohin ba su bari an fara ƙirga ƙuri'un ba kafin ranar zaɓen.

Asalin hoton, EPA
Ƙirga kuri'un da aka kaɗa ta akwatin gidan waya na ɗaukar lokaci domin sai an tantance su, ba kamar yadda mutum ke zuwa ya jefa ƙuri'a ba a gaban akwati.

An samu tasgaro kafin zaɓe
Tuni dai wannan zaɓe aka fara gabatar da shi gaban shari'a.
Domin kuwa, tun kafin zaɓen ranar Talata, an samu sama da takardun koke sama da 300 daga jihohi 44 na ƙasar da ke da alaƙa da zaɓe ta hanyar gidan waya, da kuma fara zaɓe cikin sauri a wannan shekara.
Koken da aka gabatar sun fi mayar da hankali ne kan wa'adin da aka bai wa masu zaɓe ta hanyar gidan waya da kuma karɓar ƙuri'un, an kuma buƙaci sa hannun shaidu da kuma ambulan ɗin da za a aika da ƙuri'un.
Jihohin da gwamnonin 'yan Jam'iyyar Republican ne sun bayyana cewa ya zama tilas a shawo kan matsalar maguɗin zaɓe.
Sai dai 'yan Jam'iyyar Democrats sun bayyana cewa waɗannan duk wasu matakai ne na neman hana mutane zaɓe ko kuma tauye musu 'yancinsu.

Waɗanne abubuwa ne Trump ke kokawa a kansu?
Wisconsin
Ƙwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump ya buƙaci a sake ƙirga ƙuri'un da aka jefa a jihar Wisconsin sakamakon "wasu abubuwa da ba daidai ba da aka gani" a ranar Laraba.
Babu wani tabbaci ko yaushe za a sake ƙirga waɗannan ƙuri'u, sai dai, hakan ba zai faru ba sai jami'an jihohin sun kammala tantance waɗannan ƙuri'un. Wa'adin da aka bai wa jihohi kan wannan lamarin shi ne 17 ga watan Nuwamba.
Wani farfesan shari'a daga jami'ar koyon aikin lauya ta Columbia, Richard Briffault ya bayyana cewa sai da aka sake ƙirga ƙuri'u a Wisconsin a 2016, kuma "sai da aka samu sauyi na ƙuri'u 100".
"Ƙirga ƙuri'u ba wai hanya bace ta ƙalubalantar ingancin ƙuri'a," in ji shi. "Hanya ce kawai ta tabbatar da cewa lissafin da aka yi daidai ne."
Michigan
Mista Trump ya lashe zaɓe a jihar a 2016 da ƙuri'u kaɗan - da kaɗan suka haura 10,700. A ranar 4 ga watan Nuwamba, kwamitin yaƙin neman zaɓensa ya bayyana cewa ya kai koke domin a dakatar da ƙirga ƙuri'u a jihar, duk da cewa kashi 96 cikin 100 na ƙuri'un an ƙirga su ba bisa ƙa'ida ba.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai dubban ƙuri'u da har yanzu ba a ƙirga su ba, kuma akasarinsu sun fito ne daga yankunan da tun a tarihi an san masu bin aƙidar Democrat ne, sai dai kafafen yaɗa labarai na Amurka da ma BBC na hasashen cewa Mista Biden ne zai iya lashe zaɓen.
Pennsylvania
Babban ƙalubalen a nan shi ne matakin da jihar ta ɗauka na ƙirga ƙuri'un da ya kamata a kai ranar zaɓe amma suka iso kusan kwanaki uku kafin zaɓen. 'Yan Jam'iyyar Republican na son ɗaukaka ƙara kan hakan.
Mista Weil ya bayyana cewa ya fi damuwa kan wannan matsalar ganin cewa Kotun Ƙolin ƙasar ba ta cimma matsaya ba kan lamarin kafin zaɓe.
"A ja-in-jar da aka yi da su, sun bayyana cewa sun fi so su karɓi ƙuri'un bayan zaɓen. Ina ganin cewa ƙuri'un da aka kaɗa a ranar zaɓe ta hanyar gidan waya kuma ba a samu karɓar su ba ranar Juam'a akwai yiwuwar ba za a yi amfani da su ba. Ina ganin hakan zai zama wani sakamakon ƙarya, amma ina ganin sakamakon zai na gaskiya bisa shari'a."
Shi ma Farfesa Briffault ya ƙara da cewa ƙuri'un da suka iso a makare ana ƙirga su ne daban, inda ya ce idan Mista Biden zai iya lashe zaɓen ba tare da ƙirga su ba, yana ganin babu wani amfani kai ƙara kotu.
Sai dai kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump a jihar ya ce su suka samu nasara a jihar duk da cewa akwai sama da ƙuri'a miliyan ɗaya da ba a ƙirga ba. Babu wata babbar kafar yaɗa labarai a Amurka da ta yi hasashen wanda zai lashe zaɓe a jihar ta Pennsylvania.
Georgia
'Yan Jam'iyyar Republican na jihar da kuma kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Trump sun gabatar da ƙara a gaban kotu domin dakatar da ƙirga ƙuri'u sinda suke zargin aka matsala wurin ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa ta hanyar gidan waya.
Shugaban Jam'iyyar Republican a reshen Jihar Georgia, David Shafer ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa 'yan jam'iyya da ke sa ido kan zaɓen sun shaida cewa sun ga wata mata ta "ta zuba kuri'u sama da 50 cikin wani buhu da ke ɗauke da ƙuri'un da ba a ƙirga ba da aka turo ta akwatin gidan waya.
Sun buƙaci alƙalin koyun da ya yi bincike kan ƙuri'un da aka karɓa bayan an rufe zaɓe a ranar.

Asalin hoton, Getty Images
Shin za a kai ƙara Kotun Ƙoli?
A safiyar Laraba, Mista Trump ya yi zargin cewa an tafka maguɗin zaɓe ba tare da wata hujja ba.
"Za mu je Kotun Ƙolin Amurka - muna so a dakatar da yin zaɓe," in ji Mista Trump ɗin.
Tuni dai aka dakatar da kaɗa ƙuri'a tun a ranar zaɓe a ƙasar, duk da cewa akwai tambayoyi da ake yi kan ƙuri'un da suka iso a makare. kamar na jihar Pennsylvania.
Mista Weil ya bayyana cewa: "Kotun Ƙoli ba ta da wani ƙarfi a hukumance da za ta iya dakatar da ƙirga ƙuri'un da ake yi bisa doka.

Idan aka ƙalubalanci sakamakon zaɓen, dole ne sai an samu lauyoyi domin su ƙalubalanci sakamakon a kotun jihohi.
Sai alƙalan jihohin sun amince da a sake ƙirga ƙuri'un daga nan ne za a iya buƙatar ko alƙalan Kotun Ƙoli sun sauya hukuncin kotun jihohi.
A wasu wuraren, ana sake ƙirga ne ba tare da ɓata lokaci ba idan babu tazarar ƙuri' a tsakani - idan za a iya tunawa da abin da ya faru a Florida a zaɓen shekarar 200 tsakanin Shugaba George W Bush da kuma Al Gore.

Har zuwa yaushe za a yi ta wannan harƙallar?
Sakamakon wannan zaɓen shugaban ƙasa ne, akwai wasu wa'adi muhimmai na kundin tsarin mulki da kuma na tarayya da za su iya tafiyar da abubuwa.
- Jihohi na da makonni biyar tun daga 3 ga watan Nuwamba su gano wane ɗan takara ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jiharsu. A wannan shekara, wa'adin zai ƙare ne a ranar 8 ga watan Disamba.
- Idan jiha ba ta cimma matsaya ba har zuwa wannan lokaci - a tuna cewa a ƙarshe wakilai na musamman ne ke zaɓen shugaban ƙasa ba wai ƙuri'un mutane ba - za a iya cewa ba za a yi amfani wakilan zaɓen jihohin ba yayin lissafi.
- A ranar 14 ga watan Disamba, masu zaɓen za su haɗu a jihohinsu domin su yi zaɓe.
- Idan duk da haka ba a samu wanda ya samu rinjaye ba bayan 6 ga watan Janairu, Majalisar Tarayyar ƙasar za ta gudanar da zaɓe.
- Majalisar Wakilai za ta zaɓi shugaban ƙasa sai kuma ta dattijai ta tabbatar da mataimaki. Hakan na nufin za a ga shugaban ƙasa da mataimaki daga jam'iyyu daban-daban.
- Kowane ɗan majalisa na da ƙuri'a ɗaya. Duk wanda ya samu ƙuri'a 26 shi ne sabon shugaban ƙasar Amurka.

Me ya sa ba lallai jihohi su ayyana wanda ya ci zaɓe ba?
Me zai faru idan su kansu jihohin suka kasa cimma matsaya kan su wane ne za su tsaya a matsayin wakilansu na musamman da za su yi zaɓe? Me kuke tunanin zai faru idan wata jam'iyya ta yi zargin cewa ƙuri'un da aka jefa an yi maguɗi kansu?
Manyan wuraren da ake fafatawa na North Carolina da Pennsylvania da Michigan da Wisconsin dukansu suna da bambancin gwamnati - Gwamnoni 'yn Jam'iyyar Democrat amma 'yan majalisa daga Republican akasarinsu.
A zaɓen da ake fafatawa, 'yan majalisa za su iya ɓallewa daga gwamnoninsu domin su bayar da sunayen wakilai na musamman da suke so su yi zaɓe. (Hakan ya faru a 1876.)
Majalisa ce za ta tantance waɗanda za su jefa ƙuri'ar - sunayen waɗanda gwamna ya bayar da waɗanda su 'yan majalisar suka bayar.
Idan duka majalisun dattawa da na wakilai suka amince, babu wata matsala. Idan suka kansu ya rabu, lallai ana ruwa, duk da cewa wasu masana sun bayyana cewa dokokin tarayya na goyon bayan waɗanda gwamnoni ke so

Wa'adi na ƙarshe
Koma mene ne, a ranar 20 ga watan Janairu, kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce dole ne a samu sabon shugaban ƙasa.
"Zuwa 12:00 na rana, dole ne a rantsar da wani ya zama shugaban ƙasa.
Mista Weil ya bayyana cewa zai iya yiwuwa a kasa cimma matsaya a Majalisun Tarayya kan shugaban ƙasar, amma Majalisar Dattawan za ta iya zaɓar mataimaki.
Idan har zuwa ranar rantsar da shugaban ƙasa majalisa ta kasa cimma matsaya, mataimakin shugaban ƙasar da Majalisar Dattawa ta zaɓa zai zama sabon shugaban ƙasa.
Idan kuma babu shugaban ƙasa - Kakakin Majalisar ta yanzu za ta riƙe muƙamin shugaban ƙasar. (Nancy Pelosi, 'yan Jam'iyyar Democrat).

Rahoto daga Ritu Prasad










