Zaben Amurka: Yadda Trump da Biden suka raba kan ma'aurata a Amurka

Bayanan bidiyo, Zaben Amurka: Yadda Trump da Biden suka raba kan ma'aurata a Amurka
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon yadda ma'auratan suka tafka mahawara

Yana goyon bayan Trump, tana goyon bayan Biden. Kuma ko wannensu ya yi imani da gwaninsa.

Shin aurensu zai tsira daga wannan zaɓen?

Ga ma'auratan suna ƙoƙarin sauya tunanin wasu daga hamayyar siyasa da ƙiyayya.

Suna kan manufa guda ta samar da yanayi mai kyau ga ƴaƴansu da ƙasa mai kyau maimakon caccakar juna.

Ma'auratan na ganin duk da samun saɓanin ra'ayi amma abin da ya fi muhimmanci shi ne fahimtar juna

Sun ce za a samu sauyi idan ɗan Republican zai auri ƴar Democrats kuma ƴan Democrats su auri ƴan Republicans.

Sun ce ƙaunar da suke wa juna ta ƙaru bayan muhawarar da suka tafka game da zaɓen Amurka tsakaninsu.