Zaɓen Amurka na 2020: Abin da ya sa wasu Kiristoci a Afirka ke yi wa Trump addu'ar samun nasara

Shugaba Trump

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Dickens Olewe
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Duk da kalaman batancin da ya rika furtawa a kan Afrika da 'ya'yanta, shugaban Amurka Donald Trump, na samun goyon bayan wasu kiristocin nahiyar.

''Ku sanya shi a addu'a, wato shi Trump, domin idan Allah ya baka wata dama ta jagoranci to magauta daga bangarori daban daban za su yi ta kokarin shatale ka'' in ji wani fitaccen Pasto dan Najeriya Chirs Oyakhilome.

Ya kuma yi gargadin cewa masu hamayya da shugaban na jam'iyyar Republican wanda ke neman yin tazarce a zaben kasar da ke tafe nan bada jimawa ba za su ji kunya.

''Suna jin haushinsa ne saboda goyon bayan da yake nunawa kiristoci, gara ku kwana da sanin haka, don haka da ku suke yin gaba, ku kiristoci'' in ji paston wanda wa'azin da yake gabatarwa ta talabijin ya yi kaurin suna a fadin duniya ciki har da Amurka.

Wata kur'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a watan Janairu ta nuna cewa al'ummar nahiyar musamman a kasashen Najeriya da Kenya, ba su damu da irin cin kashin da shugaban ke yi musu ba, daga ciki har da kiransu a matsayin ''Masu rayuwa a masai''.

Najeriya da Kenya kasashe ne da suka yi kaurin suna ta fuskar addini, akwai manyan coci-coci a kudancin Najeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce suna a Afrika, sannan a Kenya 'yan siyasa da dama na zuwa mujami'u don ganawa da magoya bayansu, wannan na basu damar sake yin shuhura.

Yawancin kungiyoyin kiristocin da ke wa'azin bishara a Afirka, wadanda galibinsu ke adawa da zubar da ciki, da 'yancin' yan luwadi da kuma goyon bayan Isra'ila, ba sa son magabacinsa, Barack Obama na Democrat, duk da asalinsa dan Kenya ne.

''Gwamnatin Obama ta rika kokarin yada manufar sassaucin ra'ayi a Afrika, kuma wannan abin damuwa ne ga wasu daga cikin shugabanninmu na Kiristoci, don haka abin farin ciki ne yadda gwamnatin Trump ta dakile wannan shiri'' in ji Richard Chogo, wani pasto a cocin Deliverance dake Nairobi, babban birnin Kenya.

Ya yaba wa gwamnatin Trump game da rage kudaden da take bai wa kungiyoyi, irin su Marie Stopes, wadanda ke samar da maganin hana haihuwa da kuma ayyukan zubar da ciki ba tare da shan wahala ba a kasashen Afirka da dama.

Kungiyar agajin ta soki haramcin ba da tallafin a 2017, tana mai cewa "ya jefa rayuwar mata cikin haɗari".

Yadda aka dakile fafutukar 'yancin bakaken fata

Muhawara game da 'yancin zubar da ciki ta kasance daya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a siyasar Amurka tun akalla shekaru arba'in da suka gabata.

Mayan malaman mujami'un coci na darikar Evanjalika sun hada kansu wuri guda wajen adawa da zubar da ciki, abin da ya rika yin naso hatta a tsarin siyasar kasar.

Bayan hukuncin 1973 da kotun kolin Amurka ta yanke da ya bada damar zubar da ciki 'yan Evanjalika da a lokacin ba ruwansu da duk wata sabga ta siyasa sun marawa Ronald Reagan na jam'iyyar Republican baya a zaben shugaban kasa na 1980.

Kodayake Shugaba Carter na Democrat da ke kan mulki a wannan l;okaci shima dan Evanjalika ne, 'yan wannan darika na kallonsa a matsayin mai sassaucin ra'ayi, don haka suka taimakawa abokin hamayyarsa har ya kai ga samun nasara a zaben.

Shugaba Trump tare da wasu Amurkawa bakaken fata

Asalin hoton, AFP

"Shin sauran mutanen da ba farar fata ba basu cika fuskantar wariyar launi bane a Amurka ? ko rayuwar akalla bakar fata mara karfi ta fi kyau yanzu idan aka kwatanta da shekaru bakwai da suka gabata lokacin mulkin shugaba Obama ?.

To shi dai shugaba Trump na ta yin alfahari da cewa ya yi wa Amurkawa bakake abin da babu wani shugaba da ya taba yi musu tun zamanin shugaba Abraham Lincoln,

A cewar alkalumman ma'aikatar Kwadago ta Amurka, watan da ya wuce shi ne mafi muni ta fuskar rasa ayyuka da bakaken Amurkawa suka yi tun wajajen 1970.

Ana danganta hakan ne da sauye-sauyen da annobar korona ta haifar.

1px transparent line

'Allah na son Trump'

Wata mai goyon bayan shugaban tun lokacin da yake fitowa a wani wasan kwaikwayo na talabijin ta ce duk mako tana yi masa addu'ar fatan nasara, sannan duk sa'adda ranar haihuwarsa ta zagayo ta kan wallafa sakon taya shi murna a shafukanta na sada zumunta ciki har da Facebook.

Wata babban coci a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Ta ce Allah ya mata bishara tun kafin zaben 2016 da ya samu nasara, cewa biloniyan dan kasuwan zai shiga siyasa, sannan zai tashi haikan don kare addinin kirista.

Ta ce an mata bishara da cewa ana bukatar mutum jarumi, wanda zai gudanar da rayuwar jama'a, a cewar Bintie.

''Ra'ayinsa ya saba da na masu son su rika juya rayuwar jama'a, muna son mutumin da zai kare damarmakin jama'a ne.

Shima Pasto Chogo ya amince da irin wannan ra'ayi na ta, harma ya kara da cewa ko kai ne Saddam Hussain ko Muhammad Gaddafi, ba za a rasa abu daya ko biyu da ka yiwa mutanenka na alheri ba.

Zaben Amurka na 2020

Link box banner bottom

A baya-bayan nan Mista Trump ya tunatar da magoya bayansa mabiya addinin kirista a wasu sakonnin da ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa 'yancin addini da zubar da ciki na cikin hadari idan bai yi nasara a watan Nuwamba

Amma Archdeacon Ezeji, ya fi ganin cewa lamarin ya sha banban.

"Ko ya fadi ko ya yi nasara ba abu ne da ya shafi hukuncin da ubangiji zai yanke ba''.

"Idan ya yi nasara hakan na nufin za mu ci gaba da jan zarenmu, idan kuma ya fadi hakan na nufin baza mu samu isashshen lokaci ba'' in ji shi.