Malamar cocin da ke yaƙi da fyaɗe a Afirka Ta Kudu

Asalin hoton, Reverend June Major
- Marubuci, Daga Esther Akello Ogola
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC Africa kan sha'anin mata
- An wallafa
Reverend June Major malamar coci ce da ta shafe shekaru 18 tana fafutukar tabbatar da adalci, tun lokacin da wani malamin cocin ya yi mata fyaɗe a Afirka Ta Kudu.
Ta sha shiga zanga-zangar bukatar ganin cocin Anglican ta yammacin Afirka ta bude bincike kan shari'arta da sauran ire-irensu.
A ranar 9 ga watan Agustan 2020, ranar mata a Afirka Ta Kudu, Rev Major na cikin mata da masu fafutuka da suka shanya kamfai a kan katangar gidan Archbishop din yammacin Afirka, Thabo Makgoba.

Asalin hoton, June Major
Matan sun yi zanga-zangar ce akan abin da suka bayyana da ƙin daukar isassun matakai daga cocin, kan zarge-zargen lalata kan limaman cocin Anglican da ke kudancin Afirka, ciki har da mutumin da Rev Major ke cewa ya yi mata fyade.
"Yaki na da cocin ne, kan wasu al'adu da dokokin da ake amfani da su wajen danne mata su yi shiru, wadanda suka tilasta mana shiru kuma suke ganin mu da laifi, da barin ɓata gari su ci gaba da aikata muggan laifukan da suke yi," kamar yadda ta shaida wa kafar yada labaran Afirka Ta Kudu.
Amma wannan ba shi ne karo na farko da Rev Major ke zanga-zanga kan zargin shirun da take cewa coci na yi akan irin waɗannan laifuka.
'A shirye nake na sadaukar da raina.'
A 2016, Rev Major ta shiga yajin ƙin cin abinci karo na farko.
Bayan shekara huɗu, a watan Yulin wannan shekarar, ta sake shiga yajin cin abinci, a wannan karon ta tare a kusa da gida mai lamba 20 Bishopcourt a birnin Cape Town, gidan da Archbishop Makgoba ke zaune.
"A shirye nake na mutu ta wannan hanyar, ba saboda kaina ba, ina yi ne saboda kowacce mace da yaran da aka ƙi bi wa hakkinsu," ta shaida wa BBC.
A cewar Rev Major, an kai mata harin ne a shekarar 2002, lokacin da suke hanyar ziyartar maƙabarta.
Rev Major ta ce malamin cocin ya shiga dakin da daya daga cikin iyalan malaman da suka karbi baƙuncinsu, sannan ya kai mata hari.
"Na yi kokowa da shi amma sai ya fi ƙarfina har ya shaƙe min wuya. Ban yi ihu ba saboda akwai yara a gidan. Sai ya tafi bayan ya gama abin da yake so.
"Na shiga kaduwa da mugun tsoro baya nan. Kawai na ji mutuwa nake son yi. Na kira ɗaya abokin namu na sanar da shi abin da ya faru," a bayaninta, sannan ta kara da cewa ya sake kawo mata hari a karo na biyu, kuma ya tafi lokacin da ta sanar da shi cewa ta shaidawa abokinsu cin zarafin da yake mata.
Rayuwar shiru da fargaba
Shekaru 18 da faruwa wannan lamari, Rev Major ta ce tana rayuwa cikin damuwa.
"Wata ƙawata ta shawarci mu bar zancen a matsayin sirri tsakaninmu, sannan wanda ya min fyaɗen ya alkawarta cewa ba zai sake gwada irin hakan ba.
Na amince tun da a cikin watanni kalilan kowa zai kama gabansa ya koma inda ya fito kuma ina tunanin hakan ya wadatar."
Sai dai, bayan shekara biyuu, Rev Major ta yanke hukunci bukatar cocin ta binciki al'amarin.
"Sai aka sake shawarta ta na yi shiru. Na yarda, bisa tunanin akwai bukatar na kare sunan cocin, cibiyar da nake kauna matuka. Amma kash! Wannan shiru nawa bai dawo min cikin jin dadi ba."
Rev Major ta ce tana yawaita mafarki a kullum, sannan ya kasance tana fargabar zama a dakin da ba a iya rufewa, wani lokacin tana zama a bakin kofar da bata rufuwa ta danne da bayanta.
"Ba na taɓa barin mutane su zo kusa da ni, ballantana maza, saboda mutumin da nake ganin akwai kusanci tsakanin mu ya ci zarafina," a cewarta.
Zargin coci da munafunci
Sai bayan wata wacce ta sani ta shiga irin wannan matsala ta fyade sannan Rav Major ta fito bainar jama'a da labarinta, da fatan hakan zai sama mata waraka da zaburar da mata irinta da suka fuskanci fyade su fito su kai karar wadanda suka ci zarafinsu.
Da farko ta soma gwagwarmayar nemar wa kanta adalci ta hanyar kai ƙara wajen 'yan sanda domin su yi bincike, sai dai hakan bai yi aiki ba.
Sai ta kai maganar gaban cocinsu ba wai kawai don cocin ta nema mata hakkin ba, amma ta yi tunanin hakan zai ba da dama cocin ta shawo kan matsalolin zargin cin zarafi ta hanyar lalata.
Ta ce martanin da ta samu daga cocin shi ne shiru, abin da ya harzuƙa ta shiga yajin cin abinci a karon farko a 2016. Sai a lokacin ne kawai cocin ta mayar da martini - a rana ta 7 na ƙin cin abinci, hukumomin cocin sun alƙawarta duba ƙorafinta. Sai dai, Rev Major, ta ce babu abin da ya biyo bayan alƙawarin.
Cocin ya ce ya buƙace ta ta faɗa wa ƴan sanda a sake buɗe bincike.
A ranar 1 ga watan Yuli, shekaru huɗu bayan soma hoɓɓasarta ta farko, ta ce ta ji akwai bukatar ko an tursasa mata sake shiga yajin cin abinci, bayan ta fahimci akwai munafunci daga fannin cocin.

Asalin hoton, Henry Prince
A wannan shekarar na soma yajin cin abinci, na rasa kudaden shigata a matsayin malamar coci. Ina son na koma sabon aiki a Australia da ajiye mukamin da nake rike da shi.
Sai dai, ina bukatar wasikar da za ta bayyana ko ni wace ce kafin na iya soma sabon aiki
"Wasikata ta, wadda a baya aka alkawarta, kwata-kwata ba ta Karaso ba kuma na rasa gurbin ci gaba da aiki a matsayin malamar coci tun lokacin," a cewar Rev Major. Sai ta yanke shawarar kai cocin kara kan rasa samun kudi. Har yanzu batun na kotu.
"Abin da ya fusata ni shi ne archbishop din na maganar nuna adawa da irin cin zarafin da ake nunawa mata da lalata, da fifita wani jinsi kan wani, kuma wannan dalili ne ya kawo ni nan saboda kin tabuka kommai daga cocin.
"Abin takaici ne a ce a matsayinki na mace, sai kin wuce iyaka da sa jikinki a cikin hadari, amma ina bukatar magana da Makgoba domin sanin abin da zai yi a kai, (fyade) da kuma bukatar binciken cikin gida da wasu irin adalci," a cewarta.
Abin da cocin ya ce
Kwana shida bayan Rev Major ta shiga yajin cin abinci, ta amince ta janye bayan tattaunawa da Archbishop Makgoba.
Ya ce ta gabatar da bukatarta a rubuce ta email.
"Da ranar Litinin ta zagayo, Archbishop din ya mayar min da martani inda ya ce za su soma sauraron ƙorafi kan da'a da tuntuɓar masu shigar da ƙara a inda aka aikata fyaɗen domin sake buɗe shari'ar. Kan wannan hujjar, sai na daina yajin cin abincin."
Cocin sun aike mata da saƙon email, da ke cewa "ya mayar da hankali wajen tabbatar da cewa ya shawo kan irin wadannan batutuwa ba tare da wasa ba."

Asalin hoton, Henry Prince
A shafinsa, Cocin Anglican na Afirka Ta Kudu ya ce ya shata ƙa'idojin da ofishin kowanne shugaban ya mutunta a 2002.
Wannan kuwa ƙoƙari ne na shawo kan matsaloli da dama da ake danganta da "amfani da kujerarka wajen cin zarafi da galibin lokaci ke shafar mata da yara".
A 2018, an fitar da tsare-tsaren da za su shawo kan irin wadannan ƙorafe-ƙorafe da "samar da coci mai tsaro kuma a 2019, ya sha alwashi samar da gurbin da za a ke adalci da dawo da martaba".
Sai dai, bayan shekara biyu, Rev Major da sauran masu fafutuka sun rataya bayanansu a kofar gidan archbishop din domin zanga-zanga da abin da ta kira son kai da ra'ayi da wasu mambobin kwamitin tabbatar da coci mai tsafta da tsaro ke aikatawa, wadanda kuma su din ne mambobin cocin Anglican da aka ɗorawa alhakin binciken karar da ta kai.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook Rev Major ta ce: "Na yi amanna cewa bincike da mutanen da ke kan tsarin albashi, kuma ke da alaka da coci, zai sake dilmiyar da sunana ne a matsayin mai laifi."


Ta na son binciken ya kasance wata kungiya ce mai zaman kanta za ta aiwatar. Ta tsayar da hakan da coci kuma an bata amincewar soma shirye-shiryen ganin tabbatuwar hakan.
Cocin ya fitar da nashin sanarwar, inda ya ce Rev Major tana da damar daukan lauya kuma coci a shirye yake ya taimaka mata, idan akwai bukatarr hakan.
Korafe-korafen baya
Cocin Anglican na Afirk Ta Kudu na fuskantar kararki da dama kan cin zarafi ta hanyar lalata da ake zargin malaman cocinsu
A 2018, wani marubuncin Afirka Ta Kudu da ya sha lashe kyauta, Ishtiyaq Shukri ya wallafa buɗaɗɗiyar wasika kan irin cin zarafin da ya fuskantar na tsawon shekaru a hannun wani malamin cocin Anglican yana yaro.

Asalin hoton, AFP
Archbishop Makgoba ya nemi afuwar cocin kan abin da ya bayyana da kura-kuran baya da gazawa wajen shawo kan matsalolin lalata da ake zargi.
Kwanaki bayan hakan ya sake fitowa yana bayyana cewa mutane da dama sun zo da irin wannan korafi na zargin limaman cocin na lalata.











