Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kun san kalubalen da masu lalurar laka ke fuskanta?
Yau ce ranar da aka kebe domin masu fama da lalurar laka a fadin duniya.
Makasudin ware wannan ranar shi ne domin a wayar da kan al'umma dangane da halin da masu fama da lalurar ke ciki tare da nemo hanyar tallafa musu.
Albarkacin wannan ranar ta bana BBC ta tattauna da wata mai wannan lalura wato Hajiya Hadiza Muhammad da Dakta Mamman Muhammad Lawal, kwararren likita a fannin laka da kashi a asibitin kashi na gwamnatin tarayya da ke Dala a Kano.
Hajiya Hadiza, ta bayyana wa BBC irin halin da masu irin wannan lalura ke shiga inda ta ce,"Lalurar laka lalura ce mai matukar tsanani da wahala da kuma kunci saboda rayuwace da mutum zai shige ta wadda ada yana iya yin komai da kansa, amma idan ya gamu da wannan lalura sai dai ayi masa komai".
Ta ce"Irin wannan lalura kan taba kwanyar mutum, sannan tasa shi ya shiga cikin damuwa da tashin hankali".
Don haka ne tace masu irin wannan lalura na matukar bukatar tallafi musaman daga bangaren gwamnati inda suke so a samar da kayan aikin da za a rinka kula da masu irin wannan lalura a asibitoci.
Shi kuwa Dakta Mamman, ya yi bayani ne a kan yadda ake samun wannan cuta, inda ya ce,"Yawanci bincike ya nuna cewa hadarin mota ko wani hadari a kan titi ko kuma fadowa daga bene ko wani waje mai nisa duk suke janyo mutum ya samu wannan lalurar ta laka".
Ya ce,"Akwai wadanda ke warkewa idan sun kamu da wannan lalura, kamar wadanda lakar tasu bata gama tsinkewa ba, to a kan yi musu aiki su kuma warke'.
Dakta Mamman Muhammad Lawal, ya ce ga wadanda lakarsu ta yanke gaba daya, to a gaskiya basa warkewa.
Likitan ya kara da cewa, masu irin wannan lalura na matukar bukatar kulawa ta musamman, sannan kuma yakamata a samu jami'an lafiya da zasu rinka basu shawarwari na yadda za su rinka kula da kansu da ma yadda zasu koma harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata damuwa ba.