Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juneteenth: Mece ce ita a tarihi kuma mece ce alakarta da fafutukar Black Lives Matter?
Juneteenth na daya daga cikin tsofaffin ranakun tarihi a Amurka, wadda ita ce ranar da aka kawo karshen cinikin bayin da aka shafe shekara fiye da 200 ana yi a kasar.
Ana bikin wannan rana ne a ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara tun daga 1866 kuma kungiyoyin fararen hula na Amurka kamar su NAACP sun dade suna neman a mayar da ita ranar hutu a kasar.
Har yanzu dai ba a yi hakan ba, amma jerin zanga-zangar da aka dinga yi da kuma matakin Shugaba Trump mai cike da ce-ce ku-ce a wannan shekarar ya sa an kara sanin ranar sosai fiye da baya.
To mece ce ranar Juneteenth?
An samo sunan ne daga sunan watan Yuni wato 'June' da kuma 19 ga watan wato 'nineteenth' kuma ita ce ranar da aka kawo karshen cinikin bayi a Amurka. Ana kuma kiranta da Ranar 'Yanci.
Shugaba Abraham Lincolnya ayyana Samun "yancin Kai - wanda ya sa aka 'yanta dukkan bayi - fiye da shekara biyu da aka tsara hakan.
Amma an dauki lokaci, kuma an yi hakan ne a karshen yakin basasar Amurka, kafin hakan ya tabbata.
Texas na daya daga cikin jihohin da suka shiga yarjejeniyar - wata kungiya da wasu jihohi da aka fi cinikin bayi da ta yi fafutukar nuna adawa da ba da 'yancin a yakin basasar.
Ita ce jiha ta karshe da ta mika wuya ga Kungiyar Sojin, kuma ta karshe da bakaken fata 'yan Afrika da ke Amurka suka samu 'yancinsu.
A lokacin da shugaban kungiyar Janar Gordon Granger ya karanta jawabin a birnin Galveston, yakin ya zo karshe kuma wani mai rajin a ba da 'yanci ya kashe shi a dakin taro.
Me ya sa ba a ayyana Juneteenth ta zama ranar hutu ba?
A yanzu haka, jihohin Amurka 46 cikin 50 da Gundumar Columbia suna bikin ranar Juneteenth. Amma ba ta zamo ranar hutu ta kasa ba, duk da shekarun da kungiyoyin fararen hula suka shafe suna neman a yi hakan.
A 'yan kwanakin da suk wuce, kamfanoni da dama - da suka hada da Apple da Nike da Twitter - sun shelanta cewa daga yanzu za a dinga biyan ma'aikata kudin aikin ranar a matsayin ranar hutu.
Cikin wadanda ake nunawa yatsa dangane da wariya musamman a irin wannan rana akwai hukumar kwallon kafar Amurka. An zargi NFL a 'yan shekarun nan da nuna wariya ga tsohon dan wasan San Francisco Colin Kaepernick, wanda shi ma ya sanya gwiwarsa a kasa, yayin da ake rera taken kasa a wajen gangamin Black Lives Matter.
Nikola Hannah-Jones, wata 'yar jarida ta New York Times kuma marubuciya da ta samu kyautuka da dama kan tarihin cinikin bayi a Amurka, ita ma na daga mutanen da suka shiga cikin masu kiraye-kirayen amincewa da ranar Juneteenth.
" Da yake Amurka ba ta da Ranar 'Yantar da jama'a don bikin ranar kawo karshen bautar da mutane da kuma nuna amincewa da abinda muka yi da kuma nuna ko mu su waye, to ya kamata a bayyana Juneteenth a matsayin ranar hutu ta kasa" kamar yadda ta wallafa a shafinta na twitter naran 11 ga watan Yuni.
Ta ya Trump ya janye ce-ce ku-ce kan ranar Juneteenth?
A ranar 11 ta watan Yuni, yayin da ake tsaka da zanga-zanga a titunan Amurka da dama, Shugaba Trump ya sanar da cewa shi ma zai gudanar da zanga-zanga a birnin Tulsa ranar 19 ga watan Yuni.
Baya ga ranar ita kanta, wajen da Trump din ya zaba ya janyo martani - Tulsa na daga wuraren da aka fi yi wa bakaken fata kisan kiyashi a tarihin Amurka a shekarar 1921.
Bayan 'yan kwanaki kadan Tump ya sauya shawara sannan ya mayar da gangamin na sa zuwa ranar 20 ga watan Yuni. Ya ce ba da gangan ya zabi ranar ba, kuma zai dage gangamin na sa "saboda girmamam ranar".
Sai dai bai sauya wajen gangamin na sa daga Tulsa ba - yana daya daga manyan biranen jihar Oklahoma, jihar da Tump ya samu kaso 65% na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa na 2016.
Ta ya ya Juneteenth ta danganci gwagwarmayar Black Lives Matter?
Masu fafutuka suna ta neman a kara fadakarwa kan ranar a 'yan shekarun nan, da suka hadar da wasu muhimman lamura na kasa da fafutukar Black Lives Matter ta haifar.
Yunkurin da ake yi sun hada da wani shirin talabijin na barkwanci da ake nunawa a Amurka wanda aka alakanta da Juneteenth da kuma yadda ya shafi bakake.
Daya daga shirye-shiryen da aka fara nunawa a watan Oktobar 2017 aka kuma sake nuna shi bana, ya fito fili yana bukatar a amince da ranar ta Juneteenth a matsayin ranar hutu ta kasa.
Zanga-zangar da ake ci gaba da yi yanzu da kuma wayar da kai kan wariyar launin fata sun kara kambama ranar ta Juneteenth. Akwai taruka da dama da aka shirya a duk fadin Amurka da za a gudanar a karshen mako.
Shin gwamnatin Amurka ta taba neman afuwa kan bautar bayi?
Shugaban Amurka dan jam'iyyar Democrat Bill Clinton ya nemi afuwa kan cinikin bayi a lokacin wata ziyara Afirka a 1998.
Bayan shekara goma, Majalisar Wakilan Amurka ta nemi afuwa kan cinikin bayin, da kuma shekarun da aka shafe ana nunawa bakaken Amurka wariya.
Da shekara ta kewayo kuma ita ma majalisar dattawan kasar ta nemi afuwar.
To amma wasu na ganin wannan neman afuwar ba ta wadatar ba. Akwai kiraye-kiraye da ake yi a Amurka kan cewa a biya jikokin bakaken da aka bautar diyya, to amma batun ya janyo rarrrabuwar kai. Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a bara ta nuna cewa 74% na bakaken Amurka sun goyi bayan biyan diyyar, yayin da 85% na farare kuma suke adawa da biyan.