Covid 19: Wa ya fi dacewa ya rufe baki da hanci?

    • Marubuci, Daga Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Edita kan harkokin Lafiya, BBC News online
  • An wallafa

Takunkumin kariya da safar hannu da sauran abubuwa na taimaka wa jama'a wajen dakile yaduwar cutar coronavirus - to sai dai ya kamata ayi amfani da su yadda ya dace.

Wasu mutanen na amfani da takunkumin kariya da aka yi a gida - su ma al'ummar Amurka ana shawartar su da su rinka amfani da takunkumin kariyar a yayin shiga cikin jama'a. To sai dai abin tambaya a nan shi ne ko ya kamata hakan?

Me ya sa jama'a ke amfani da takunkumin kariya?

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi duba ga shaidun baya-bayan nan da suka hada da ko za a sauya tunani kan kwayar cutar.

Hukumar ta so ta sake yin nazari kan ko akwai wani alfanu a sanya takunkumin kariya ga kowa da kowa.

Kwararru sun yanke cewa ya kamata a bar wa ma'aikatan lafiya takunkumin kariya da suke sanyawa a lokacin gudanar da ayyukansu, inda hakan ke nufin na gama-gari ne ba.

Mutane iri biyu ne kawai ya kamata su sanya takunkumin kariya:

  • Maras lafiya wanda kuma yake dauke da alamun coronavirus
  • Mai kula da wadanda ake zaton suna dauke da coronavirus

Ba a amince wa dukkan jama'a sanya takunkumin kariya ba saboda wadannan dalilan:

  • Takunkumin ka iya gurbata sakamakon tari da atishawa da wasu mutane suka yi a lokacin sanya ko cire takunkumin.
  • Yawaita wanke hannu da bayar da tazara tsakanin mutane sun fi sanya takunkumin alfanu wajen kare kai daga cuta.
  • Idan mutum ya rufe fuska hakan ka iya janyo zargin ko mai laifi ne

Cutar coronavirus dai na yaduwa ne ta hanyar feshi daga atishawa ko tarin mutanen da ke dauke da cutar.

Irin wannan feshin na shiga jikin dan adam ta hanyar idanu ko hanci ko kuma baki, watakila kai tsaye daga mai cutar ko kuma bayan mutum ya taba wani abu da mai kwayar cutar ya gurbata.

Shin ya ya ingancin takunkumin da ake yi a gida yake?

An bai wa 'yan Amurka shawarar yin amfani da tsumma mai tsafta domin rufe fuskarsu a lokacin da suke cikin jama'a. Jami'an lafiya sun ce takunkumin kariya da ma'aikatan lafiya ke sanyawa na karanci saboda haka ya kamata a bar musu.

Maras lafiya ko kuma mai jinyar mai dauke da cutar coronavirus su ne kadai aka fadawa su sanya takunkumin kariya. To sai dai jami'an Amurka na fatan sabbin dokokin ka iya dakatar da mutanen da ba su da alamun cutar yada cutar ba tare da sun sani ba.

To sai dai yin amfani da tsohon tsumma bai dace ba kuma hakan kan iya kara yiwuwar kamuwa da cutar, in ji masana na Tarayyar Turai.

Sun ce akwai yiwuwar kwayoyin cutar ka iya ratsa tsumman. Har wa yau, idan tsumman a jike yake cutar ka iya samun mafaka.

Birtaniya dai ba ta bai wa jama'a shawarar amfani da takunkumin na kariya walau dai na tsumma ko kuma wanda ma'aikatan lafiya ke amfani da shi.

Wane takunkumin fuskar ne yafi kowanne?

Akwai takunkumin fuska iri daban-daban a asibitoci kuma kowanne yana da amfaninsa inda ya dace. Kuma wanda yafi kowanne kariya shi ne samfurin FFP3 ko kuma N95 ko FFP2.

Masana ba sa bai wa jama'a shawarar amfani da takunkumin na fuska ba. Wadanda ke tare da masu dauke da cutar cornavirus ne ke amfani da irin wadannan takunkumai na fuska.

Wane abu ne kuma yake kariya ga coronavirus?

Hukumar Insorar Lafiya ta Birtaniya na kwarara wa jama'a gwiwa wajen yin amfani da safar hannu da sauran abubuwan da ake sanyawa domin kariya daga cornavirus.

Bugu da kari, an shawarci ma'aikata da ke aikin ceto su sanya cikakkun kayan kariya kamar safar ta hannu da takunkumin da gilashin ido.

An kuma gargadi mutanen gari da su guji sanya safar hannu da sauran kayan kariya kamar takunkumin fuska da gilashin ido na neman kariya daga cutar coronavirus.

Hukumar Insorar Lafiya ta Birtaniya, NHS, ta bai wa jama'a shawarwari kamar haka:

  • Wanke hannu da ruwa da sabulu a kai-kai na akalla dakika 20 da kuma da zarar mutum ya koma gida.
  • Yin amfani da man goge hannu na sanitizer idan ba a samu ruwa da sabulu ba.
  • Rufe baki da hanci da tolifefa ko kuma cikin gwiwar hannu - amma ba tafin hannu ba - a lokacin da mutum yake tari ko kuma atishawa.
  • Jefa tolifefar da aka yi amfani da ita a cikin kwandon shara tare da wanke hannaye.
  • Ka da a taba idanu ko hanci ko kuma baki da hannu har sai an wanke su.