Bikin nuna al'adun gargajiya na Lumiere a London

An wallafa

An kawata wasu daga cikin fitattun wurare a birnin London da hasken wuta da ado saboda bikin nuna al'adun gargajiya na Lumiere

Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Za a kawata wasu daga cikin fitattun wurare da fitilu a birnin London, da suka hada da Patrice Warrener inda za a yi adon fitilu masu kaloli a mutum-mutumin da suke wajen, wanda yake shiyyar Westinster Abbey, saboda gabatowar ranar bikin al'adu ta Lumiere.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Za a kawata wurare talatin da adon fitilu a yankunan Piccadilly da Mayfair da King's Cross da dandalin Trafalgar da kuma Westminster.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Za a fara taron ne wanda shi ne ma fi girma da ba a taba yin irinsa ba a birnin, daga misalin karfe 6.30 na yamma agogon GMT zuwa 10.30 na dare agogon GMT na kowacce rana har zuwa 17 ga watan Janairu. Adon fitilu na fitar hankali kamar an watso su daga sama za su cika sararin samaniyar dandalin St James, inda a nan ne mahalarta za su yi dandazo.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, A kan titin Regent kuwa za a saki butum-butumin wata katuwar Giwa ne a sararin samaniya.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Mahalarta a Oxford Circus za su ga wani zanen hadari mai kala da Janet Echelman ta yi zai dinga yawo a sama.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Shi kuwa wannan akwatin kifayen Benedetto Bufalino da Benoit Deskill ne suka ajiye shi a dandalin Grosvenor. A kan tarho ne a ajiye a wajen, amma yanzu an dasa akwatin kifaye cike da kananan kifaye masu rai kalar ruwan gwal.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Wannan biki dai wasu masu shirya shiri na Artichoke ne suka shirya shi, wadanda su ne suka shirya makamancinsa a Durham da ke arewacin Ingila. Duk da cewa suna da ma'aikata da yawa, amma sai da suka sake neman ma'aikatan sa kai daga London domin su taimaka musu wajen jagorantar mutane da kuma dasa abubuwa.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Daraktar Artichoke Helen Marriage, ta shaida wa BBC cewa, "Kallon wannan abin armashi dai kyauta ne ba mai biyan ko taro." Akwai kuma tsibirin da aka yi da roba wanda ba na gaske ba, wanda kuma wani kamfani na Sipaniya Luzinterruptus ne ya kirkishe shi, da shi ma za a gani a dandalin Trafalgar.
Adon fitilu a birnin London
Bayanan hoto, Akwai ma wani shiri na Brothers and Siters da Ron Haselden ya hada, wanda za a nuna shi a dandalin Grosvenor.