Sarkin Zulu ya bukaci a zauna lafiya
An wallafa
A Afirka ta Kudu, sarkin 'yan kabilar Zulu yayi tir da hare-haren da ake kaiwa 'yan ci-rani, inda akalla mutane bakwai suka hallaka.
Tashin hankalin ya barke ne bayan da sarki Goodwill Zweletheni ya bukaci baki da su fice daga Afirka ta Kudun.
To amma a cewarsa an juya kalaman nasa.
A wannan rahoton na Bilkisu Babangida, watakila ba zaku ji dadin ganin wasu hotunan ba