Jawabin kwatar 'yanci a Washington

An wallafa

Cikar shekaru 50 da shaharraren bakar fatan Amurka, marigayi Martin Luther King, ya gabatar da jawabinsa wanda yayi fice a duniya wato " I have a dream " a wani gangami a birnin Washington a 1963.

Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Hotunan da Leonard Freed ya buga a litaffin "This is the Day:The March on Washinton" wanda ake nuna wa bukin cika shekaru hamsin da jawabin Martin Luther King
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Tare da sauran ayyukan da bakaken fata Amurkawa suka gabatar, za a iya kallon hotunan da Freed ya dauko a kan Martin Luther King a wajen karatu na tunawa da margayin a Washington DC
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Masu fafutukar kwato 'yanci a bukin da aka yi a ranar 28 ga watan Agustan shekarar 1963
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Fiye da Amurkawa 200,000 ne suka shiga maci a Washington DC don neman adalci ga dukkan Amurkawa.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Farar fata da bakake duk sun saurari fitaccen jawabin Martin Luther King mai taken"I Have a Dream" wanda ke bayani a kan 'yanci da daidaito a Amurka.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Ya yi jawabi a kan bukatar a daina nuna wariyar launin fata da nuna bambamci tsakanin farare da bakake a Amurka.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Rabaran King ya yi aiki tukuru don kawo karshen wariyar launin fata ba tare da zubar da jini ba, sannan kuma a tabbatar da adalci tsakanin al'umma.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, A shekarar 1964, Majalisar dokoki ta amince da dokar 'yancin 'yan kasa wacce ta kawar da wariyar launin fata, da bambamcin addinni da kuma jinsi a Amurka.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, 'Yan sa'o'i kafin macin, mai daukar hoto Freed ya nuna hotunan inda mutane ke daukar kwalayen nuna goyon baya ga bukatar 'yanci.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, 'Yan sanda sun zagaye ko'ina, sannan mutane na wucewa kusa da gida mai tarihi na Lincoln wanda ke dauke da rubutu " House Where Lincoln Died" wato 'Gidan da Lincoln ya mutu'.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Mutane sun yini rike da hannun juna a macin da su ke neman kwatarwa kansu 'yanci.
Washington DC, 28 ga watan Agusta,1963
Bayanan hoto, Duka hotunan an same su ne daga Estate of Leonard Freed – Magnum Photos (Brigitte Freed) kuma Getty Publications ne ya wallafa.