Rigakafin cutar zazzabin cizon sauro
An wallafa
Cutar zazzabin cizon sauro ko maleriya ta kasance babbar matsala a daruruwan kasashe.
A Afrika, maleriya na kashe yaro daya cikin ashirin kafin su kai shekaru biyar da haihuwa, kuma ya zuwa yanzu ba a samu riga-kafin cutar ba.
Sai dai binciken da wadansu masana suka gudanar a Amurka ya nuna cewa ana samun sakamako mai kyau ta hanyar amfani da haske na musamman.