Yadda farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Abuja

Bayanan bidiyo, Bidiyon farashin raguna a kasuwar raguna ta Abuja
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A yayin da ya rage kwana 4 kafin babbar sallar layya ta shekarar 2022, abokiyar aikinmu, Sadiqa Bkeke, ta leka babbar kasuwar raguna ta Dei-Dei da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

A bana, masu saye da sayarwa duk su na kokawa kan tsadar dabbobin layya musamman raguna da aka fi amfani da su wajen yin layyar.

Tawagar BBC tayi kicibis da Mallam Muhammad wani da ya je kasuwar domin ya sayi rago amma ya shafe kusan yinin ranar gaba daya bai saya ba saboda tsadar dabbobin.

Muhammad ya ce "farashin raguna ya fi yadda na yi tsammani, bara kamar wannan lokacin ragon da na saya Naira dubu 80 zuwa 90 ya koma dubu 140 a bana".

Shi ma Sarkin kasuwar dabbobi ta Dei-Dei Alhaji Abdullahi Abdulkadir ya tabbatar da tsadar ta raguna inda ya ce akwai sauyin farashi a bana idan aka kwatanta da bara sannan ya bayyana dalilai da suka kawo tsadar raguna sosai.

"Yanayin tsadar kudin mota daga inda ake dauko dabbobi sakamakon tsadar man dizel da kuma tsadar dusa su ne manyan dalilai da suka kawo tsadar raguna a bana" in ji Alhaji Abdullahi.

Ya kara da cewa buhun dusa daya ya kai Naira dubu tara zuwa dubu 10 maimakon dubu hudu a baya.