BBC ta bankado yadda ake safarar yara masu larurar nakasa a Tanzania
An wallafa
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Tawagar ma'aikatan BBC da ta yi shigar-burtu ta bankado yadda ake safarar mutane masu fama da laurar nakasa daga Tanzania zuwa Kenya.
Galibin yaran da aka yi safara, an dauke su ne daga hannun iyayensu, bayan an yi musu alkawarin cewa za su samu rayuwa mai inganci.
Amma sabanin haka, an tilasta wa kananan yaran su rika yin bara a kan totuna – tsawon shekaru – inda su kuma mutanen da suka dauke su suna cin riba.
Shirin BBC Africa Eye ya taimaka wa daya daga cikin yaran ya tsira.
Njeri Mwangi ta aiko mana da wannan rahoton daga Nairobi.