Ƴar arewacin Najeriya da ta shiga jerin fitattun mutane na duniya na 2022

Bayanan bidiyo, Ƴar arewacin Najeriya da ta shiga jerin fitattun mutane na duniya na 2022
An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fatima Babakura, wata matashiya ce ƴar Najeriya da take da sha'awar haɗa kayan ƙawa na al'ada, amma a zamanance.

Sunanta ya shiga jerin fitattun mutane na Mujallar Forbes na 2022 na ƴan ƙasa da shekara 30.

Fatima tana fito da sunan Afirka ta hanyar ayyukan wani kamfani mai suna Timabee da ke yin kayayyakin ƙawa.