Yadda ɗaruruwan mutane ke rububin ɗiban ruwa a wata ƙatuwar rijiya a Indiya

Bayanan bidiyo, Yadda ɗaruruwan mutane ke rububin ɗiban ruwa a wata ƙatuwar rijiya a Indiya
An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mutanen ƙauyen Khadimal a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya na cikin tsananin takurar rashin ruwa, inda suke sa rayuwarsu a haɗari kullum don samun ko da bokiti ɗaya ne na ruwa.

Ƙauyen, wanda yake yankin Amravati mai fama da matsanancin fari a gundumar Vidarbha, na yawan fama da tsananin zafi akai-akai.

Mazauna yankin sun ce hukumomin ƙauyen kan aika tankar ruwa biyu ko uku kullum a juye a rijiyar, inda nan da nan sai mutane su fara rububin ɗiba don cika mazubansu.

Matsalar na ƙamari ne saboda rashin kyan ruwan da tsaftarsa – yara na yin rashin lafiya idan suka sha.

Bayan da sashen BBC Marathi ya wallafa wannan bidiyon, Avishyant Panda – shugaban gundumar Amravati – ya ziyarci ƙauyen ya kuma ce gwamnatin za ta ƙara yawan ruwan da ake kai wa a tankokin.

Sannan ya ce za su yi ƙoƙarin shimfiɗa bututu don kawo ƙrshen matsalar ƙrancin ruwa a ƙauyen.