Taimakon da ya kamata a bai wa mata masu fama da matsaloli lokacin al'ada

Bayanan bidiyo, Matsalolin da mata suke fama da su a lokutan al'adarsu
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Masana harkokin lafiyar mata sun bayyana cewa wasu mata suna fama da larurori daban-daban yayin da suke yin jinin al'adarsu.

Wata kwararriyar likitar mata, Dr Badia Maje Sayyadi, ta shaida wa BBC cewa kashi tamanin zuwa casa'in cikin dari na mata suna fama da larurori yayin al'adarsu amma kasa da kashi ashirin ne na mata suke fama da larurori masu tsananin da "za su shafi mu'amalarsu da mutane."

Ta kara da cewa larurorin da mata kan yi fama da su lokacin al'ada sun hada da ciwon kai, ciwon mara da yawan fada da sauransu.