Bidiyon sharhi kan takarar wasu ƴaƴan ƙusoshin Najeriya
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An kammala zaɓukan fitar da gwanaye na jam'iyyun siyasa a Najeriya, a matakin gwamnoni da ƴan majalisar dokoki na jiha da na tarayya da ƴan majalisar dattijai.
Kazalika babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta kammala nata zaɓen fitar da gwanin har a matakin shugabana ƙasa, yayinda jam'iyya mai mulki ta APC za ta yi nata a mako mai kamawa.
Za a iya cewa zaɓukan sun wuce amma sun bar ƴan Najeriya da ci gaba da tattauna yadda suka kasance, tun daga matakin rawar da daliget suka taka, da ma yadda wasu manyan masu riƙe da muƙamai suka sha ƙasa.
Sannan an ga yadda wasu sabbin ƴan takarar da suka kasance ƴaƴan wasu ƙusoshin ƙasar suka yi nasarar lashe wasu matakai na zaɓukan fitar da gwanin, yayin da wasu takwarorin nasu kuma suka sha kaye.
A wannan bidiyon, Umaymah Sani Abdulmumin ta yi duba kan wasu ƴaƴan wasu manyan ƙusoshin Najeriya da suka yi nasara a zaɓukan fitar da gwanaye na jam'iyyun siyasar ƙasar.
Waɗanda suka yi aikin bidiyon:
Tsarawa da shiryawa: Umar Rayyan
Gabatarwa: Umaymah Sani Abdulmumin
Daukar bidiyo da tacewa: Fatima Othman