Labarin wata yarinya da aka yi wa auren dole a Chadi

Bayanan bidiyo, Labarin wata yarinya da aka yi wa auren wuri a Chadi
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A duk dakika biyu, ana yi wa mace daya auren wuri, a cewar wata kungiya da ke rajin kare hakkin mata mai suna Girls Not Brides.

Kasar Chadi da ke tsakiyar Afirka na cikin kasashen da aka fi yi wa mata auren wuri a duniya.

Duk da wata sabuwar doka da aka kafa a 2015, wadda ke neman kawar da auren wuri zuwa 2020, amma lamarin na ci gaba da faruwa.

Emery Makumeno ya ziyarar N'Djamena, babban birnin ƙasar ta Chadi, domin gano dalilin hakan.