Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Garba Tudun Wada Gombe

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Garba Tudun Wada Gombe
An wallafa

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Malam Garba Tudun Wada a Gombe haifaffen jihar Sokoto ne kuma a can ya taso, daga baya ya koma Gombe inda ya yi karatuttukansa da kuma harkokin da'awa da wa'azi.

Ya fara karatu tun daga na farfaru da babbaƙu a wajen wani malami Malam Buba na makarantar allo. BAyna nan kuma ya yi "saukar zuƙu" daga nan ya yi karatu a wajen Mlaam Muhammadu Basakkwace.

Bayan da ya koma Gombe ya kafa makarantar koyar da yara alkurani. A duk lokacin da malam Basakkwace ba ya nan malam Garba ke koyar da yara, amma a lokacin da yake nan to shi ma yana daga cikin masu koyo, in ji shi.