Ana fargaba kan makomar mutanen da suka makale a mahakar ma'adinan a Burkina Faso

Bayanan bidiyo, Ana fargaba kan makomar mahakan ma'adinan da suka makale a Burkina Faso
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Ana ci gaba da neman ma'aikatan hakar ma'adinai takwas da suka makale a karkashin kasa tsawon makonni hudu a wani wajen hakar ma'adanin zinc da ke Burkina Faso.

'Yan kasar Burkina Faso shida da dan Zambia daya da kuma dan kasar Tanzania sun makale a karkashin kasa bayan wani mamakon ruwan sama ya mamaye wurin hakar ma'adinai na kamfanin Perkoa na kasar Canada.

Wakiliyar BBC Lalla Sy ta hada mana wannan rahoton: