Aissatou Faye: Matashiyar da ta yi arziki da kiwon shanu a Senegal

Bayanan bidiyo, Aissatou Faye: Matashiyar da ta yi arziki da kiwon shanu
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Wata matashiyar manomiya 'yar kasar Senegal ta bayyana yadda noma da kiwo suka sauya rayuwarta.

Aissatou Faye, wadda ta yi karatun boko a fannin kasuwanci da kudi a Senegal da Amurka, ta shaida wa BBC cewa kiwon shanu yana taka muhimmiyar rawa a rayuwarta.

Ta kar da cewa iyayenta ne suka sanya mata sha'awar kiwo ko da yake da farko ba ta sha'awa.