Sanata Kabiru Marafa: Zaluncin APC ne ya sa muke tunanin fita jam’iyyar

Bayanan bidiyo, Zaluncin APC ne ya sa muke tunanin fita jam’iyyar – Sanata Marafa
An wallafa

Danna hoton sama domin kallon bidiyon

Sanata Kabiru Marafa ya ce jam’iyyun siyasa da dama ne ke zawarcinsu, bayan abin da ya kira zaluncin da APC ta yi masu.

Sanatan ya shaida wa BBC cewa “Gaskiya jam’iyyu da yawa sun nemi mu suna son mu taka karagar motarsu domin kai wa ga biyan bukatu na siyasa.”

Wannan na zuwa bayan jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta ce kofarta a buɗe take ga Sanata Marafa da kuma tsohon gwamna Abdul’ziz Yari Abubakar.

Sai dai Marafa ya ce ba su kai ƙarshen sauya sheƙa ba, yana mai cewa riga malam Masallaci ne PDP ta yi.