'Abin da ya sa muka kirkiro manhaja domin tallafa wa marasa karfi a watan Ramadan'
An wallafa
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Wata kungiya ta kirkiro wata manhaja mai suna GivFreeAfrica da zummar taimaka wa mabukata abinci a watan Ramadam.
Aisha Bashir, matashiyar da ta kirkiro manhajar, ta ce sun kirkiro manhajar ce domin bai wa masu abin-hannu damar samun hanyar taimak wa mabukata da abin da za su ci.
"Akwai mutane da dama da ba su da abin da za su ci, akwai kuma masu hali da dama da ba su san yadda za su taimaka ba, ko sun sani ba su da lokacin da za su taimaka din. Shi ya sa muka kirkiri wannan application din.
"Mun hada mabukata da masu hali da kuma masu sayar da abubuwa domin su rika mu'amala."
Ta kara da cewa manhajar ta saukaka yadda mabukata suke samun taimako.