Bidiyo: Makahon da ya kera mota a Najeriya

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Makahon da ya kera mota a Najeriya
An wallafa

Dannata hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Abdul'aziz Balogun wani matashi ne da ke da larurar makanta a Jihar Legas da ke kudancin Najeriya.

Amma hakan bai hana shi neman ilimi ba inda ya karanta fannin injiniyan jiragen sama.

A tattaunawarsa da BBC, matashin ya ce ya kera mota domin ya nuna wa jama'a cewa bai kamata larurar makanta ta hana kowa cika burinsa na rayuwa ba.