Yadda ake wahalar ruwa a sassan birnin Kano

Bayanan bidiyo, Yadda ake wahalar ruwa a sassan birnin Kano
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Duk da cewa Kano na da dam-dam masu dimbin yawa, matsalar karancin ruwan sha na ci gaba da ci wa al'ummar birni da kewayen jihar tuwo a kwarya.

Hukumomi a jihar dai na cewa suna yin bakin kokarinsu wajen samar da wadatacce sannan kuma tsaftataccen ruwan sha.

Sai dai alamu na nuna akwai jan aiki a gaban hukumomin kasancewar birnin Kano na kara fadada sannan kuma bututun ruwan bai kai wurare da dama ba.

Yara 'yan makaranta ba sa samun zuwa makaranta ko kuma ba sa zuwa da wuri sakamakon fadi-tashin neman ruwa.