Gidan-yarin Roumieh: Yadda tabarbarewar tattalin arzikin Lebanon ta shafi babban kurkukun kasar

Bayanan bidiyo, Yadda tabarbarewar tattalin arzikin Lebanon ta shafi babban kurkukun kasar
An wallafa

Latsa hoton da ke sma domin kallon bidiyon:

A halin yanzu Lebanon tana fama da tabarbarewar tattalin arziki mafi muni a tarihinta kuma hakan yana shafar gidajen-yarinta.

Mutanen da ke tsare a kurkukun da 'yan uwansu suna kokawa kan rashin yawa da ingancin abincin da ake ba su.

Daga rashin ingancin abinci da rashin kula da lafiya, Lebanon - kasar da ba ta iya ciyar da sojojinta- tana fama wajen kula da fursunoninta.

Rashin gudanar da shari'a a kan lokaci yana ta'azzara halin da fursunoni suke ciki.

Sashen Larabci na BBC ya samu damar shiga gidan-yarin Roumieh, kurkuku mafi girma a kasar.