Ramadan: Amfanin azumi ga lafiyar jiki

Bayanan bidiyo, Ramadan: Amfanin azumi ga lafiyarmu
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Baya ga fa’idar azumi a addinance, masana lafiya na cewa azumi yana da fa’ida ga lafiyar ɗan-Adam.

Masanan kuma sun bayar da shawara kan irin lokaci da nau’in abincin da ya kamata mai azumi ya ci lokacin buda-baki.

Nau’ukan abincin sun haɗa da abu mai zafi da ƴaƴan itace da ganyayyaki da kuma ruwa.

Aisha Sharif Baffa ta tattauna da masaniyar lafiyar abinci, Zainab Ujudud Shariff.