Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Usman Isa Taliyawa

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Sheikh Usman Isa Taliyawa
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Malamin addinin Musuluncin nan na Gombe Sheikh Usman Isa Taliyawa ya ce su suka soma kafa Fitiyanul Islam a Kano zuwa Gombe, karkashin jagorancin Modi Salga da Aliyi Alkali.

Sheikh Usman Taliyawa wanda ya shafe tsawon shekaru yana koyarwa da da'awa ya ce ba shi da wani buri a yanzu ganin ya rabu da duniya cikin imani da rufin asiri.

Malamin wanda shi ne mataimakin Bala Lau shugaban kungiyar Izala ya shaida haka ne a shirin Ku San Malamanku na BBC.