Binciken BBC: Yadda cin hanci ke taka rawa wajen haddasa haɗurra a kan titunan Kenya

Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon binciken BBC kan yadda cin hanci ke haddasa haɗurra a titunan Kenya
An wallafa

Latsa hoton sama ku kalli bidiyon binciken BBC:

Shin titunan da suka ratsa ciki da wajen Kenya sun zama tarkon mutuwa ne?

Tsakanin 2020 da 2021, waɗanda suka mutu a kan titunan Kenya sun ƙar da kashi 20 cikin 100.

A shekarar da ta gabata, mutum 4,500 ne suka mutu sannan aka raunata fiye da 16,000.

Gwamnatin Kenya ta ce bugaggun direbobi da lodi fiye da kima da gudun wuce kima na cikin dalilan da suka fi haddasa haɗurra.

Amma ko cin hanci da rashawa ma na cikin dalilan?

Ɗan jarida Richard Chacha, wanda shi ma ya ji rauni a wani hatsarin mota a Kenya, ya bi tawagar sashen binciken ƙwaƙwaf ta BBC wato Africa Eye wajen fallasa masu karɓar rashawa wajen bai wa 'yan ƙasa lasisin tuƙi.