Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi gasar cin ganyen latas tsakanin zomo da wata mata a Amurka
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An yi wata gasa ta cin ganyen latas tsakanin wani ƙaton zomo da wata mata.
Wani kantin sayar da abinci ne a Amurka ya shirya gasar tsakanin zomon mai suna Honey “Mega” Bunny da matar mai suna Raina Huang.
A ƙarshe dai matar ce ta yi nasara bayan da ta cinye kilo 1.5 na latas din yayin da shi kuma zomon ya kasance cikin rashin sha’awar cin ganyen a ranar da aka yi gasar.