Yadda yakin Ukraine ya sa duniya ta manta da yakin Yemen, inda aka kai hari 700 a wata guda
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A yayin da hankalin duniya ya koma kann yaƙin Ukraine kacokam, a Yemen kuwa yaƙin da aka shafe shekaru ana yi a ƙasar ne ke ƙara muni.
Hukumomin agaji na ta gargaɗi cewa miliyoyin mutane na fuskantar barazana a ƙasar, kuma a wannan watan ne ake cika shekara takwas da fara yaƙin.
A watan Maris kaɗai an kai hare-haren sama fiye da 700 a Yemen.