Me ake nufi da hana jirage shawagi da kasashen yamma ba sa son sa wa a Ukraine?

Bayanan bidiyo, Me ake nufi da hana jirage shawagi da kasashen yamma ba sa son sa wa a Ukraine?
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ukraine ta nemi ƙasashen yamma da su duba yiwuwar sanya dokar hana jirage shawagi a sararin samaniyar ƙasarta don hana Rasha kai hare-hare ta sama.

Amma duk da hare-haren da Rashar ke kai wa unguwannin mutane da ke jawo ƙaruwar mutuwar fararen hula, ƙasashen Yamman ba sa wata hoɓaɓasa ta danya dokar hana jirage shawagin.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi gagaɗi cewa zai kalli duk wani ƙoƙari na ƙaƙaba dokar hana jirage shawagi a Ukraine a matsayin takalar yaƙi.

Me ake nufi da Me ake nufi da dokar hana jirage shawagi kuma me ya sa kasashen yamma ba za su sa dokar a Ukraine ba?

Wannan bidiyon ya yi bayani dalla-dalla.