Duniya na bukatar ganin annan - yadda mata ke haihuwa a fagen yaki

Bayanan bidiyo, Duniya na bukatar ganin annan - yadda mata ke haihuwa a fagen yaki
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon:

Dr Yuri German likitan mata ne da ke aiki a birnin Kherson, garin da ya zama filin dagar Rasha bayan kutsen da ta yi wa Ukraine.

Yana ci gaba da taimakon mata su haihu a yayin da ake cikin yaƙin, daga wani asibiti da ke kusa da wajen da ake yawan kai harin bam.

Wannan bidiyon na ɗauke da bayanai kan halin da mata masu haihuwar ke ciki.