Ukraine: Bidiyon dawowar kashin farko na 'yan Najeriya gida
An wallafa
Kashin farko na 'yan Najeriya da suka tsere wa yakin da ake yi a Ukraine ya isa filin jirgin saman Abuja, babban birnin kasar ranar Juma'a da safe.
Shugaban kwamitin harkokin waje a Majalisar Wakilan Najeriya Yusuf Buba ya shaida wa BBC dalibai 451 ne suka iso kasar.
Yana cikin jami'an gwamnatin kasar da suka je Bucharest, babban birnin Romania domin taho da 'yan kasar ta Najeriya.