Ku San Malamanku da babban Limamin Gombe Malam Muhammadu Umar Pindiga
Ku latsa hoton da ker sama don kallon bidiyon:
A wannan makon shirin Ku San Malamanku ya tattauna ne da Malam Muhammadu Umar Pindiga daga jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.
Malam Pindiga shi ne babban Limamin Gombe a Masallacin Ƙofar Fada.
Malamin haifaffen garin Pindiga ne a jihar Gomben, kuma ya ce an fi saninsa da Alhaji Dukku.
Sai dai ya ce bai san taƙamaiman lokacin da aka haife ba amma wani aminin babansa wanda ya ci sunansa ya gaya masa cewa an haife shi ne ranar ɗaya ga watan Yunin 1946 amma wani bangaren ya shaida masa a 1948 aka haife shi.
Mahaifinsa ya yi limanci a Pindiga tsawon shekara 30 don haka a wajensa ya fara karatu.
A cikin wannan bidiyon dai malamin ya bayyana gwagwarmayar karatunsa da irin littattafan da ya karanta da sauran dawainiyar rayuwa.