Bayani dalla-dalla kan mamayar Rasha a Ukraine a kwanaki bakwai na farko
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga kalaman Putin, hare-haren makamai masu linzami, da kuma jajircewar Ukraine da kira a gwabza yaƙi.
Dubban mutane sun mutu a makon farko na mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine kuma a cewar hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya kusan mutum 900,000 sun tsere daga kasar.
An sanya takunkumai a kan Rasha sannan kasashen duniya suna ta zanga-zanga.
Wannan shi ne jerin abubuwan da suka faru a makon farko na mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine