Yakin Ukraine: Manyan illolin makaman nukiliya

Bayanan bidiyo, Yakin Ukraine: Manyan illolin makaman nukiliya
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojin da ke lura da makaman nukiliyar kasarsa su shiga shirin ko-ta-kwana a yakin da kasar ke yi da Ukraine.

Hakan ne ya jefa duniya cikin fargaba game da yiwuwar harba makaman na nukiliya, lamarin da ka iya yin matukar illa ga kasashen duniya.

Shugaban hukumar makamashi ta Najeriya, Yusuf Aminu, ya yi mana bayani kan illar makaman nukiliya.