Yakin Ukraine: 'Mijina ya tsaya ya yi yaki, ni kuma na bar kasarmu'

Bayanan bidiyo, 'Mijina ya tsaya ya yi yaki, ni kuma na bar Ukraine'
An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

An tilasta wa mata da kananan yara su fice daga Ukraine yayin da mazajensu da kuma iyayensu suka tsaya a kasar domin yin yaki da dakarun Rasha.

Matan suna neman mafaka a kan iyakar Poland.

Mazajensu sun ba su sako karara: su gudu ku tsira, mu kuma za mu tsaya mu fafata a yaki da dakarun Rasha.