Bayani dalla-dalla kan Shugaba Putin na Rasha

Bayanan bidiyo, Bidiyon bayani dalla-dalla kan Shugaba Putin na Rasha
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Da alama Shugaban Rasha Vladmir Putin ya bai wa mutane mamaki da ya afka wa Ukraine, wanda shi ne babban matakin soja da ya ɗauka tun bayan ƙwace yankin Crimea a 2014, amma fa bai taɓa ɓoye manufarsa ba ta faɗaɗa tasirin Rasha.

Mista Putin wanda ya yi karatun aikin lauya a jami'a, ya kasance a kan mulki tun 2000 - a matsayin shugaba da kuma firaminista kuma shi ne shugaban da ya fi kowa daɗewa a Fadar Kremlin tun bayan jagoran kama-karya na Tarayyar Soviet Joseph Stalin, wanda ya mutu a 1953.

Wata ƙuri'ar raba-gardama da aka kaɗa a 2020 ta bai wa Putin damar ci gaba da mulki fiye da wa'adin mulkinsa na yanzu wanda zai ƙare a 2024. Saboda haka, zai iya ci gaba da zama a mulki har zuwa 2036.

Amma ta yaya ya zo nan? Ga bayanai game da harkokin siyasa da rayuwar mutumin da a yanzu duk duniya ke ta magana a kansa.