Yakin Ukraine: Mata sun koma masu haɗa bam ɗin kwalba a Ukraine

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A ranar da Vladimir Putin ya bai wa dakarunsa umarnin shiga Ukraine, Arina ta yi shirin koyar da rawa bayan ta koma daga aiki da kuma holewa.

Kwana uku bayan haka, malamar ta harshen Turanci ta mayar da hankali wajen haɗa bam ɗin kwalba wato Molotov a wani wurin shaƙatawa.

Birnin Dnipro da ke kudancin Ukraine, bai fuskanci hare-haren dakarun Rasha ba, ya zuwa yanzu, amma mazaunansa suna shirin kare kansu.

Wasu bidiyon masu alaƙa da za ku so