An shawarci ƴan Ukraine da ka da su ruɗe, su 'tunkari Rasha kawai'

Bayanan bidiyo, An shawarci ƴan Ukraine da ka da su ruɗe
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ƴan Ukraine na cikin ruɗun neman mafita ta ko dai su gudu ko su ɓuya ko kuma su tsaya su tunkari Rasha a yayin da ta fara yaƙar ƙasarsu.

Hare-haren da Rasha ke ta kai wa ƙsar ya durƙusar da al'amura tare da jawo asarori daban-daban.

Amma shugaban ƙasar Ukraine ya bai wa ƴan ƙasar shawara da ka da su ruɗe sanna su ɗauki makamai don kare kansu daga Rasha.