Rikicin Ukraine: 'Yadda karar bama-baman Rasha ta tashe mu daga bacci'
An wallafa
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Wasu 'yan Najeriya sun bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki bayan Rasha ta soma kai hari a Ukraine.
Wata matashiya 'yar Najeriya da ke karatu a Ukraine, Fiddausi Mohammed Usman, ta shaida wa BBC Hausa yadda suka wayi gari cikin zulumi sakamakon hare-haren da sojojin Rasha suka kai a kasar.