Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Muhammadu Idrisa
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A wannan makon shirin Ku San Malamanku ya tattauna ne da Malam Muhammadu Idrisa daga Gombe.
An haifi Malam Muhammad Idrisa a jiihar Gombe arewa maso gabashin Najeriya, kuma ya fara karatun a hannun mahaifinsa Modibbo Idris Biri, wanda daga baya Allah ya yi masa rasuwa tun lokacin yana da karamin shekaru.
Bayan rasuwar mahaifin malam Muhammadu Idrisa ne kuma daga nan a unguwarsu ta Jeka-da-fari aka kai shi wata makaranta ta wani malami da ake kira malam Yahuza wanda shi ma daga baya Allah ya yi masa rasuwa.
Daga nan in ji malamin ya taba karatun babbaku da farfaru, da kuma karatun Alkura'ani wanda ya ce har ya kai har izu biyar.