Na'urar da ta taimaka wa mutumin da jikinsa ya shanye ya samu haihuwa

Bayanan bidiyo, Na'urar da ta taimaka wa mutumin da jikinsa ya shanye ya samu haihuwa
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

David M’zee na da shekara 22 a lokacin da ya yi wani hatsari da ya lalata masa ɓargo da ƙashin baya, shekara 12 da suka wuce.

A shekarar 2017 aka yi masa dashen wata na'ura da take taimaka masa yake iya tsayawa da tafiya a hankali.

Ya ce na'urar ta taimaka wa rayuwarsa sosai ta yadda har ya yi aure ya samu haihuwa.

Ga labarinsa a cikin wannan bidiyon da wakilin BBC kan Kimiyya Pallab Ghosh ya ruwaito.

Wanda ya shirya: Emily Selvadurai.

Daukar bidiyo: Julius Peacock.

Tacewa: Aisha Doherty