Rayan: Yadda aka yi jana'izar yaron da ya mutu a rijiya bayan shafe kwana huɗu a cikinta
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ɗaruruwan ƴan Moroko ne suka taru a wajen jana'izar yaron nan Rayan mai shekara biyar da ya faɗa rijiya ya shafe kwana huɗu a cikinta kafin daga bisani ya rasu.
Rayan Oram ya faɗa rijiya mai zurfin mita 32 ranar 1 fa watan Fabrairu, inda aikin cetonsa ya zama mai wahala.
Lamarin ya jawo hankalin mutane a ko ina a fadin duniya inda aka yi ta fatan a ciro shi a raye, sai dai hakan bai yiwu ba.